
Mohammed Shehu, Mai Baiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Shawara kan Harkokin Jiha ya sauya sheƙa zuwa ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau a Jam’iyar APC a Jihar Kano.
Da ya ke jawabi a gaban dubban ƴan jam’iya a ƙarshen makon da ya gabata a Kano, Shehu ya ce ya yanke shawarar komawa ɓangaren Shekarau ne, tare da dubban ƴan jam’iya, sakamakon mulkin kama-karya da Abdullahi Abbas ke yi a jam’iyar.
Shehu ya baiyana cewa shi da masoyansa sun yanke shawarar ci gaba da yi wa Sanata Barau Jibrin yaƙin neman zaɓen gwamna da ya ke nema.
“kowa ya san mu muke da ɗumbin masoya a ƙaramar hukumar Nassarawa, amma duk da haka sai shugabancin Abdullahi Abbas su ka kasa gane hakan, sai su ka goyawa waɗanda ba su da magoya baya a siyasa baya.
“Bari in faɗa muku cewa ba fa mu kadai bane a tafiyar nan. Akwai masu muƙami a gwamnati da kuma sauran ƴan siyasa da su ke goyawa tafiyar jagorancin Ɗanzago baya, kuma mu mun fi amincewa da yaƙin neman zaben gwamna na Barau Jibrin.
“Sanata Barau ɗan takara ne mafi inganci wanda kowa shi ya ke yi. Ba wai ƙaƙabawa mutane shi a ka yi ba, sai dai ma al’ummar Kano ne ke son su ƙaƙabawa kansu shi,” in ji Shehu.
Tun bayan da kotu ta tabbatar da shugabacin jam’iya na Ahmadu Haruna Ɗanzago a ke samun wasu na jikin Ganduje su na ficewa zuwa tsagin Shekarau.
Daily Nigerian Hausa ta gano irin su Tsohon Mataimakin Gwamna, Farfesa Hafizu Abubakar da na jikin Ganduje, Murtala Zainawa cikin waɗanda su ka sauya sheƙa zuwa ɓangaren na Shekarau.