
Alhaji Kabiru Usman Sanka ya rasu a yau talata.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Usman ya rasu bayan wata rashin lafiya da har yanzu ba a kai ga baiyana ta ba.
Kafin rasuwarsa, muryar marigayin sananna ce a gidajen rediyon Kano ga ma’abota jin fitaccen karatun tafsirin alƙur’ani mai girma na Marigayi Sheikh Isa Waziri.
Muryar marigayin ta yi suna, musamman a shekaru sama da ashirin da su ka gabata sakamakon yadda ya ke yawan faɗin “Allah Ya saka da alkhairi, dan Kashiful Gummati”.