
Nuradeen Shehu, wani mai gadi a wata makaranta mai zaman kanta dake kan titin Danmusa, Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale a jihar Kano, ya rataye kansa.
Kwamishinan ƴansandan jihar, Hussaini Gumel, ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a daya daga cikin ajujuwan makarantar.
Ya ce a safiyar Lahadi, 28 ga watan Janairu, wani Abdullahi Abdulsalam mazaunin Rijiyar Zaki ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa mai gadin ya rataye kansa da igiya a cikin wani aji.
CP din ya bayyana cewa tawagar ƴansanda daga reshen Gwale, karkashin jagorancin DPO din Gwale, su ka garzaya wurin da lamarin ya faru, inda sai da su ka ɓalle kofar ajin sannan su ka samu damar shiga.
An ce ƴansandan sun kai mai gadin zuwa babban asibitin Murtala Mohammed inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Daga bisani aka mika gawarsa ga iyalansa domin yi masa jana’iza.
An bayyana cewa Shehu ya rataye kansa ne saboda tsohuwar matarsa ta sake yin wani auren.
Kwamishinan yansandan ya ce rundunar ta fara bincike kan lamarin.