
Ana sa ran za a rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alkalin Alƙalai na Ƙasa, CJN, bayan murabus ɗin Mai Shari’a Tanko Muhammad.
A tuna cewa Tanko ya yi murabus daga mukaminsa ne bisa rahotannin rashin lafiya ne, a cewar wata sanarwa da mataimaki na musamman na CJN kan harkokin yada labarai, Isah Ahuraka ya fitar.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa da kuma sauran laifuka a kan CJN ɗin da ƴan uwansa alkalan Kotun Ƙoli 14 su ke yi masa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Ariwoola ne mafi girman muƙami bayan mai shari’a Mary Odili ta yi ritaya a ranar 12 ga watan Mayu bayan ta kai shekaru 70 da haihuwa.
Shi ma Ariwoola, a 2028 a ke sa ran zai aikin shari’a.
An naɗa Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alkalin Kotun Kolin Najeriya a shekarar 2011.