
Manoma 43 da aka zaɓo daga ɓangarori daban-daban na mazabar Anambra ta Gabas da Yamma l, da su ka ɗauki horon noman rani a ƙasar Egypt ne za su amfana da tallafin Naira miliyan 1 kowannen su domin fara harkar noma.
Chinedu Obidigwe, mamba mai wakiltar mazabar Anambra ta gabas da yamma ne ya bayyana haka a Aguleri, Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas, lokacin da mambobin Kungiyar Cigaban Aguowulu, APU, suka tabbatar da goyon bayansu gare shi da ya tsaya takara a karo na biyu a yau Talata.
APU kungiya ce ta hazikan matasa daga Enugu-Otu, Mkpunando da Eziagulu-Otu duk a Garin Aguleri dake Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas.
Obidigwe ya ce an zaɓo waɗanda suka ci gajiyar tallafin ne daga sassa daban-daban na mazaɓar domin samun horo kan dabarun noman rani a Masar.
Ya ce Kananan hukumomin Anambra ta Gabas da Anambra ta Yamma suna da albarkar ruwa kuma an ba su tallafin ne don tabbatar da samar da abinci a duk shekara da kara yawan kayan noma da kuma fitar da ɗumbin iyalai daga kangin talauci.