Home Siyasa Ƴan Majalisa 18 Cikin 22 sun amince da tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mahdi

Ƴan Majalisa 18 Cikin 22 sun amince da tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mahdi

0
Ƴan Majalisa 18 Cikin 22 sun amince da tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mahdi

 

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta jefa ƙuria’r amincewa da tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau daga kan muƙaminsa da gagarumin rinjaye.

A yayin wani zama a jiya Alhamis, ƴan majalisa 18 cikin 22 ne suka amince da ɗaukar matakin, yayin da ɗaya tak ya ƙi amincewa.

Haka nan, ‘yan majalisar sun nemi Alƙalin-Alƙalai na Zamfara, Mai Shari’a Kulu Aliyu ya kafa kwamatin da zai binciki Mahdi bisa zargin saɓa sashe na 190 da 193 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa dangantaka tsakanin mataimakin gwamnan da Gwamna Bello Muhammad Matawalle ta yi tsami tun lokacin da gwamnan ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC a bara, amma Mahdi ya ci gaba da zama a PDP.