
Kimanin zawarawa 500 ne a jihar Kaduna aka baiwa tallafin Naira miliyan 37 na kasuwanci don ciyar da kansu da iyalansu.
Matan da aka zabo daga mazabu 22 na mazabar Kachia/Kagarko, an ba su Naira 30,000 kowacce, yayin da wadanda suke da sana’ar su a hannu aka ba su tsakanin N300,000 zuwa N500,000.
Da yake jawabi a wurin rabon, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kachia/Kagarko ta jihar Kaduna, Gabriel Saleh Zock, ya bayyana cewa hakan na daga cikin kokarin rage wahalhalun da ake fuskanta a kasar nan.
Zock ya ce duk wacce sana’arta ta bunkasa nan da shekara ɗaya za a kara bata takkafin Naira miliyan 1.
A cewarsa, “Mun zo nan ne domin karfafa wa malaman addini a wannan wata na Ramadan ga al’ummar Musulmi da kuma lokacin rance ga Kiristoci. Don haka na ga ya dace in nuna goyon bayana ga malaman addini kuma na roke su da su sadaukar da lokacinsu da yi wa kasa addu’a domin a samu zaman lafiya.”
Tun da farko, Darakta daga Cibiyar Zaman Lafiya da magance rikice-rikice, Chukwuemeka Mba, Daraktan Horaswa na CMB, Kenneth Okoro da Barista Abdulkadir Bello Idris sun gabatar da kasidu kan cin zarafi na Jinsi (GBV) da yadda mata da al’umma za su iya dakile wannan annoba.