Home Labarai Ɗan majalisa ya yi tattaki a Abuja kan garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Ɗan majalisa ya yi tattaki a Abuja kan garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

0
Ɗan majalisa ya yi tattaki a Abuja kan garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

 

A yau Laraba ne dai ɗan majalisar wakilai, Bamidele Salam, mai wakiltar Mazaɓar Ede North/Ede South/ Egbedore na jihar Osun a ranar Laraba a Abuja ya gudanar da wata zanga-zanga shi kaɗai, inda ya ke kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ceto fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da aka sace.

Tun ranar 28 ga watan Maris aka sace fasinjojin a cikin jirgin kasan.

Ya caccaki Buhari kan yadda ya bar wadanda aka ɗauke ɗin a hannun wadanda suka sace su.

Ɗan majalisar wanda ke dauke da kwalayen ya yi tattaki babu takalmi daga shahararriyar Unity Fountain zuwa harabar majalisar dokokin kasar, ya koka kan halin da mutanen da aka kama suke ciki.

Dan majalisar ya rubuta a kwalayen na sa cewa, “Shugaba Muhammadu Buhari, don Allah ka kara himma wajen samar da ‘yanci ga wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin ƙasar Abuja zuwa Kaduna da sauran ‘yan kasa da ake garkuwa da su.

Bamidele ya ce, yin garkuwa da mutanen da aka kashe da kuma kashe su, wani barna ne ga lamirin kasa da gwamnatin da ke da alhakin tabbatar da rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma yi kira ga Shugaban kasa da ya tashi tsaye wajen ganin an ceto wadanda abin ya shafa cikin gaggawa da kuma larura.