
Majalisar Dattawa ta hori Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da ta tabbatar da cewa zaben 2023 ya kasance sahihi ba tare da rikici da maguɗi ba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana haka a jiya Talata, a jawabinsa na maraba kan dawowar zaman majalisar bayan hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
Lawan ya bukaci alkalan zaben da su kasance kan gaba wajen ganin cewa zaben ya cika burin ‘yan Najeriya.
“Babu uzuri. INEC ta samu duk abin da ta nema na gudanar zaɓe.
“Mun sake sadaukar da kanmu wajen ganin mun goyi bayan INEC da duk wata hukumar gwamnati da ke kokarin tabbatar da sahihin zabe a wannan shekara da ma bayan ta.
“Muna kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan dama ce ta zaben wanda suke so.
“Tabbas, mun yi imanin cewa ƴan kasa sun yi daidai ta hanyar samun katin zabe na dindindin (PVCs) saboda idan baku da PVC, ba za ku iya yin zabe ba,” in ji shi.
Lawan ya ce majalisar ta yi gagarumin aiki ta hanyar gyara dokar zabe.
“Aikin zabe kamar yadda aka tsara a yau, zai samar da kyakkyawan sakamako na zabuka,” in ji shi