Home Kanun Labarai Majalisar dattawa ta tsiyace – Inji Bukola Saraki

Majalisar dattawa ta tsiyace – Inji Bukola Saraki

0
Majalisar dattawa ta tsiyace – Inji Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewar a yanzu haka halin da ake ciki majalisar dattawa ta shiga tassku sakamakon tsiyacewa da asusunta yayi.

Saraki ya bayyana haka ne, ya bayyana hakan ena wata sanarwa da mai taimaka masa akan kafafen yada labarai ya sanyawa hannu, bayan da ya kai ziyara zuwa ga Shugabannin da mambobin hukumar gudanarwa ta majaalisar dattawa.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a lokacin da yake amsa tambayar Shugaban hukumar, Adamu Fika,inda yace ya kamata hukumar ta samu matsuguni na dindindin, inda Shugaban majalisar ya sha alwashin samarwa da hukumar matsugunin ta kanta, duk kuwa da cewar a yanzu majalisar ta tsiyace.

Yace batunkudi shi ne babbar matsalar majalisar dattawa yanzu haka, inda yace, rashin kudaden gudanarwa yana damun majalisar sosai.

“Daya daga cikin abinda yake damun mu shi ne batun kasafin kudin hukumar”

“Haka kuma, abinda akasarin ‘yan Najeriya suke zato shi ne majalisar datawa tana da dumbin kudaden gudanarwa,amma dai abin ba haka yake ba”

“Kamar yadda muke aiki a  karkashin kudurorin da muka zartar, da yawan wasu kudurorin da muka zartar sun kasa kammaluwa sabida rashin kudaden gudanar da su”

Daga nan yayi  kira ga SShugabannin majalisar da su taimaka da ‘yan kudade domin samun gudanar da wasu ayyukan dake bukatar kudade.