Home Siyasa Majalisar dokokin Jihar Adamawa ta tsige mataimakin kakakin majalisa da wasu mutum uku

Majalisar dokokin Jihar Adamawa ta tsige mataimakin kakakin majalisa da wasu mutum uku

0
Majalisar dokokin Jihar Adamawa ta tsige mataimakin kakakin majalisa da wasu mutum uku
Gwamna Bindow Jibrilla na Jihar Adamawa

Majalisar dokokin jihar Adamawa a ranar litinin ta tsige mataimakin kakakin majalisar dokokim jihar Mista Sunday Peter da shugaban masu rinjaye Musa Muhammad.

Sauran wadan da aka tsige din sun hada da mataimakin shugaban masu rinjaye Mutawali Mohammed da kuma shugaban marasa rinjaye, Justina Nkom ‘yar jam’iyyar SDP dake wakiltar mazabar Lamude.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewar, Kabiru Mijinyawa ya jagoranci zaman majalisar na farko bayan da suka dawo daga hutun makwanni shida.

An zabi sabon mataimakin kakakin majalisar Mista Emmanuel Tsamdu mai wakiltar Madagali daga jam’iyyar APC, sannan kuma an zabi Hassan Burguma dan majalisa mai wakiltar Hong daga jam’iyyar APC a matsayin sabon shugaban masu rinjaye.

Dan majisa Abubakar Hayatu daga APC ne ya gabatar da kudurin wannan tsigewa yayin da dan majalisa mai wakiltar Mubi ta kudu ya goyi bayan kudurin.

Sannan majalisar kuma, ta zabi Abubakar Isa dan majalisa mai wakiltar Shelleng daga APC a matsayin sabon mataimakin masu rinjaye, yayin da Lamsumbani Dili daga PDP ya zama sabon shugaban marasa rinjaye.