Home Labarai Majalisar Dokokin Jihar Kano na yunkurin tsige Kakakinta, Ata

Majalisar Dokokin Jihar Kano na yunkurin tsige Kakakinta, Ata

0
Majalisar Dokokin Jihar Kano na yunkurin tsige Kakakinta, Ata

Daga Hassan Y.A. Malik
‘Yan majalisar dokokin jihar Kano suna yunkurin tsige kakakin majalisar, Alhaji Abdullahi Yusuf Ata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano.

Wani mijiya na Daily Trust ya bayyana ma ta hakan a daren jiya a yayin da a yanzu haka ‘yan majalsa 21 sun rattafa hannu a bisa kan takardan don goyon bayan a kan tsige kakakin majalisan.
Mijiyar taa tabbatar da cewa a halin yanzu an tsige manya jami’an majalisar biyo bayan rattaba hannu da ‘yan majalisar 21 suka yi a takardar tsige

“Mun riga mun tsige wasu manya manyan jami’an majalisar biyo bayan da ‘yan majalisan 21 sun rattafa a bisa kan takardar tsige su sannan a halin yanzu muna bukatar karin ‘yan majalisa 6 wadanda idan an samu hakan an samu kaso 2 a cikin 3 kafin mu iya tsige kakakin majalisar.”

An tambaye shi a kan dalilin da ya sa ake yunkurin tsige kakakin majalisar, mijiyar ya ce, “dalilan na da yawa amma babban dalilin da ya sa ake so a tsige shine rashin iya aikinsa. Kakakin na mayar da majalisar baya.

“Ba mu iya gudanar da zama sai karfe 2:00 na rana sannan kuma abubuwa ba su tafiya kamar yadda ya kamata. Ba za mu iya ci gaba da zama a hakan ba saboda mun kasance wakilai masu wakiltar jama’ar mazaban mu.” shi ya maye gurbin Alhaji Kabiru Alhassan Rurum, wanda yayi murabus daga kujerar a watan Yuni a shekarar da ta gabata a kan ana masa zargin cin hanci da rashawa.