
Ɗan majalisar dokokin jihar Legas, Abdulsobur Olayiwola Olawale ya rasu.
Ɗan majalisar, wanda aka fi sani da Omititi, shi ne wakilin mazaɓar Mushin II a jihar ta Legas
Rahotanni sun ce ɗan majalisar ya yanke jiki ya faɗi, ya kuma rasu a filin wasa na Rawang Pam Township da ke Jos, a jiya Talata.
Ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.
Omititi ya kasance shugaban kwamitin majalisar akan ayyuka na kananan hukumomi.
A jiya ne dai ɗan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya kaddamar da yakin neman zabensa na 2023 a jihar Plateau.