
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da gyaran dokar jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kano, Wudil ta 2021.
Ƴan majalisar, a zaman da su ka yi a yau Talata, wanda shugaban majalisar, Hamisu Chidari ya jagoranta, sun amince da sauya sunan jami’ar zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote.
Hakan ya biyo bayan wata wasika da bangaren zartaswa ya aika wa majalisar a watan Mayu, inda ya nemi amincewar sauya sunan jami’ar zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, ADUST, Wudil.
Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewa da rahoton da kwamitin majalisar kan ilimi mai zurfi ya yi.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Madari, (APC-Warawa) ne ya gabatar da kudirin amincewa da kudirin, inda Nuhu Acika (APC-Wudil) ya mara masa baya.
Ƴan majalisar dai sun kaɗa kuri’ar amincewa da kudirin bayan karatu na uku.
Da yake zanta wa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman, Madari ya bayyana cewa amincewar ta biyo bayan nasarorin da Dangote ya samu da kuma gudunmawar da ba su misaltuwa ga ilimi da ci gaban jihar da kasa baki daya.
Shugaban majalisar ya umurci magatakardar majalisar da ya mika wa gwamnan kudirin don ya rattaba hannu a kai.
A shekarar 2008, tsohon Gwamna Ibrahim Shekaru ya nada MDangote a matsayin uba ga jami’ar, sannan Gwamna Abdullahi Ganduje ya sake nada shi a shekarar 2021.