Home Labarai Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da fara gina shaguna a asibitin zana

Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da fara gina shaguna a asibitin zana

0
Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da fara gina shaguna a asibitin zana

 

 

 

Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta bada umarnin dakatar da shirye-shiryen fara gina shaguna a jikin Asibitin Kula da Cututtuka Masu yaɗuwa, IDH, wanda a ka fi sani da asibitin zana a jihar.

Wannan matakin ya biyo bayan wani ƙudiri na gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar Mazaɓar Ƙaramar Hukumar Fagge, Tukur Muhammad ya shigar gaban majalisar a zamanta na yau Laraba.

Da ya ke magana da manema labarai bayan zaman majalisar, Muhammad ya ce akwai zargin cewa za a ɗauke babbar kofar shiga asibitin, wacce ke kan titin France Road, a maida ita kan hanyar zuwa Whether Head duk sabo da fara ginin shagunan.

Ɗan Majalisar, wanda ya sauya sheƙa da ga jam’iyar PDP zuwa NNPP, ya ce al’umma za su sha wahala wajen zuwa asibitin idan a ka maida kofar shiga ta koma kan hanyar Whether Head, wacce ya ƙara da cewa ta shiga lungu.

A cewar sa, ya shigar da ƙorafin ne domin rashin dacewar gina shagunan, inda ya nuna gamsuwa da matakin Majalisar na dakatar da ginin.

Ya kuma baiyana cewa majalisar ta kafa wani kwamiti, wanda shima yana ciki, domin bincike da kuma hana irin wadannan gine-ginen a jihar.