Home Labarai Majalisar Dokokin Kano ta naɗa sabon mataimakin kakakinta

Majalisar Dokokin Kano ta naɗa sabon mataimakin kakakinta

0
Majalisar Dokokin Kano ta naɗa sabon mataimakin kakakinta

 

 

Majalisar Hokokin Jihar Kano ta zaɓi Kabiru Dashi, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kiru kuma ɗan jam’iyar APC a matsayin mataimakin kakakinta, bayan murabus ɗin Zubairu Massu, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyar NNPP.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa zaɓen na Dashi ya biyo bayan amincewa da shi da da Sale Marke, APC-Dawakin-Tofa, ya yi ne a zauren majalisa a yau Litinin.

Nuhu Achika, APC-Wudil ne ya goyi bayan ƙudurin, bayan ƴan majalisar sun tabbatar da zaɓensa a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.

Nan take darakta mai kula da harkokin shari’a na majalisar, Nasidi Aliyu ne ya rantsar da Dashi a zauren majalisar a zaman da kakakin majalisar Hamisu Chidari ya jagoranta.

Chidari ya taya Dashi murnar zabensa tare da ba shi tabbacin goyon bayan majalisar.

Dashi, a jawabinsa na amincewa da zaben, ya yabawa gidan bisa ganin ya cancanci wannan sabon naɗin.