
A yau Alhamis ne Majalisar Taraiya ta tabbatar da nadin Farfesa Saleh Abdullahi Usman a matsayin shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON.
Hakan ya zama cewa Farfesa Usman shi ne shugaban NAHCON na 6.
Tabbatarwar ta zo ne bayan da kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar Dattawan ta tantance shi a ranar Talata.
A wata sanarwa da Fatima Usara, kakakin NAHCON ta fitar a yau Alhamis, tabbatarwar ta nuna irin yarda da kwarewa Farfesa Usman Wajen aikin da aka bashi.
Shi ma kuma ya nuna godiya ga majalisar tariya bisa wannan tabbatarwa inda ya nuna kwarin gwiwa yin aiki tuƙuru don tabbatar da yarda da aka yi da shi wajen yin aikin.