
Ana zaman ɗar-ɗar a Jihar Zamfara yayin da majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Mataimakin Gwamna, Mahadi Aliyu.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa raikici ya ɓarke tsakanin Mataimakin Gwamnan da Gwamnan jihar, Bello Matawalle sakamakon ya ƙi bin gwamnan su koma jam’iyar APC tare.
A wata sanarwa a Gusau ranar Juma’a, Babban Daraktan Hulɗa da Manema Labarai da kuma Jama’a na majalisar, Mustafa Jafaru-Kaura, ya ce matakin ya biyo bayan gabatar da ƙudirin tsige Mahdin da Mataimakin Kakakin Majalisa, Malam Nasiru Magarya ya yi.
“Kamar yadda sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 wanda ya baiwa ‘yan majalisa ikon tsige gwamna ko mataimakinsa bisa zargin karya kundin tsarin mulki, aikata laifuka ko kuma zubar da kimar mukami.
“Saboda haka, a yau mataimakin shugaban majalisar kuma shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati ya gabatar da buƙata a hukumance tare da sanar da Shugaban Majalisar shirye-shiryen tsige Barr. Mahdi Aliyu Muhammad Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar,” in ji Kaura.
“Mataimakin shugaban majalisar ya zargi mataimakin gwamna Mahdi Aliyu-Gusau da laifin karya kundin tsarin mulki, zubar da kimar muƙami da kuma almundahanar kuɗaɗe, wadanda dukkansu laifuka ne da za a tsige shugaba a kan aikata su.
“Ya kuma kara da cewa sashe na 188 na kundin tsarin mulkin 1999 ya basu ikon fara yunkurin tsige mataimakin Gwamna ba tare da bata lokaci ba.”
A nashi jawabin, shugaban majalisar ya yi alkawarin cewa majalisar za ta duba zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan tare da ɗaukar mataki daidai da yadda kundin tsarin mulki ya tanada.