Home Kanun Labarai Majalisun Dattawa da na wakilai sun amince da kasafin kudin shekarar 2018

Majalisun Dattawa da na wakilai sun amince da kasafin kudin shekarar 2018

0
Majalisun Dattawa da na wakilai sun amince da kasafin kudin shekarar 2018

Majalisun dokoki da na dattawa sun amince da kasafin kudin shekarar 2018, sai dai sun kara shi da Naira biliyan 500.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar musu da kasafin kudin Naira tiriliyan 8.6, yayin da ‘yan majalisun suka maida kasafin kudin ya koma Naira Tiriliyan 9.1, watanni shida bayan an gabatar da kasafin kudin gaban hadakar zaurukan majalisun dokokin.

Shugaban kwamitin dake kula da sha’anin kasafin kudi na majalisar dattawa, Danjuma Goje yace anyi wannan karin ne a cikin kasafin kudin bayan da aka tattauna batun hakan da ‘yan majalisar zartarwa Shugaban kasa.

Yace anyi hakan ne, bayan da aka kara adadin kudin da aka sanyawa gangar man fetur daga dala 45 zuwa 51.

Haka kuma an amince da musayar dalar amurka akan Naira 305 tare da tono gangar gurbataccen mai miliyan 2.3 a kowacce rana, kamar yadda ‘yan majalisar zartarwa ta Shugaban kasa suka amince.