
Majalisun Dattawa da takwararta ya wakilai sun dage dawowa zaman majalisun biyu sakamakon rasuwar wani dan majalisar wakilai Funke Adedoyin.
Ana sa ran barkewar dambarwa a yayin Zaman majalisun biyu sakamakon sauya sheka da Shugabannin majalisun Bukola Saraki da Yakubu Dogara suka yi daga APC zuwa PDP.
Akwai dai tarin ayyukan da suke gaban majalisun da suke bukatar duba su. Akwai batun kasafin kudin hukumar zabe ta kasa INEC wadda majalisar dattawa zata tattauna akai da kuma batun amincewa ko jin amincewa da kasafin.
Kana kuma, akwai batun ciwo bashin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dattawa ta sahale masa ciwowa domin yin wasu ayyuka.
Wadannan da ka wasu je ake sa ran za a tattauna daga zarar majalisun sun dawo bakin aiki.