Home Labarai Makarantar Ƴansanda ta buɗe shafin ɗaukar ɗalibai

Makarantar Ƴansanda ta buɗe shafin ɗaukar ɗalibai

0
Makarantar Ƴansanda ta buɗe shafin ɗaukar ɗalibai

Makarantar ƴansanda ta Najeriya ta bude shafin yanar gizo na ɗaukar ɗalibai karo na 10 ga masu sha’awar nema.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya kuma kara da cewa aikin rajistar ta yanar gizo zai dauki tsawon makonni shida, daga ranar 24 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Satumba.

Adejobi ya ce shiga makarantar zai baiwa ƴan Nijeriya maza da mata masu kyawaun hali damar yi wa kasa hidima.

A cewarsa, masu nema dole ne su kasance yan asalin Nijeriya ta hanyar haihuwa kuma su mallaki lambar shaidar kasa, NIN, da kuma sakamakon jarrabawar JAMB ta 2023, da maki da bai gaza 180 ba.

Kakakin ƴansandan ya ce tabbas dalibi ya zabi makarantar horar da ƴansanda ta Najeriya, Wudil, a matsayin zaɓin farko a fom din JAMB.

Ya ce kuma mai nema dole ne ya mallaki mafi karancin maki shida da bai wuce zama biyu a jarrabawoyin WAEC da NECO ko makamancinsu ba, tare da samun maki a Turanci da Lissafi.

Adejobi ya ce dole ne mai neman ya kasance tsakanin shekaru 17 zuwa 21 kafin ranar 31 ga watan Oktoba kuma ya kasance cikin koshin lafiya, jiki da kuma ƙwaƙwalwa.

“Mai nema kada ya zama kasa da tsayin maza 1.67m, mata kuma 1.64m, tare da fadin girman kirjin da bai gaza kasa da 86cm (inci 34) ba, na maza kawai.”