
Hassan Y. A. Malik
Shugaban majalisar dattijan Nijeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki, a jiya Talata ya bayyana cewa da dama daga cikin wadanda ke rike da madafun iko a wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari, makiyan dimokuradiyya ne.
Saraki ya bayyana hakan ne a zaman majalisar ta jiya, a yayin da ya ke karin bayani game da koken da Sanata Dino Melaye ya gabatar a gaban majalisar, akan yadda gwamnatin tarayya ta maka shi a kotu bisa zargin wai ya bawa ‘yan sanda bayanin karya game da koken da ya shigar a shekarar da ta gabata a gaban hukumar ‘yan sanda na cewa wai wasu mutane da ya ambata sunansu na son daukar rayuwarsa.
A yayin shigar da koken, Melaye ya ce, gwamnatin tarayya ta dauki hukuncin gurfanar da shi a gaban kuliya ne kawai don yana kalubalantarta, inda ya kara da cewa babu wata barazana daga gwamnati ta hannun ministan shari’a Abubakar Malami, da za tsorata shi ko ya hana shi fadin abinda ya hakikance shi ne gaskiya.
Gwamnatin tarayya, ta bakin ministan shari’a Abubakar Malami, a ranar Lahadin da ta gabata, ta shelanta gurfanar da Sanata Melaye a gaban kotu a ranar Alhamis, 1 ga watan Maris, 2018, bisa abinda ta kira bayar da bayanin kanzon kurege ga ‘yan sanda tare kuma da yin kazafi ga shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kogi, Mista Edward Onoja, na wai ya yi yunkurin kashe shi (Melaye).
Meleye ya bayyana wa zauren majalisar yadda wasu ‘yan bangar siyasa suka yi yunkurin kashe shi a cikin garinsu, cikin jihar Kogi. Meleye ya ce, ya kai rahoto ga ‘yan sanda, kuma aka bukaci da ya bayyana sunayen wadanda ya ke zargi da kai masa harin, inda ya bayyana wa ‘yan sanda sunayen wadanda ‘yan bangar suke ihu sunayensu, “Sai Edward, sai Edward, sai Edward”.
Melaye ya ci gaba da cewa ko kafin ya ambaci sunayen wadanda ya ke zargin ga ‘yan sanda sai da ya yi la’akari da irin tsananin rashin jituwa da ya ke tsakaninsu da wadannan mutane ya tabbatr da cewa za su iya yin komai don su ga baya raye bisa furuce-furucen da suka yi a baya game da shi.
“Yan sanda sun gabatar da bincike kuma sun samu abubuwa da dama da suke nuna da hannun wadanda na ke zargi a yunkurin kisa na, wanda hakan ne ma ya sanya aka gurfanar da su a kotu a jihar Kogi”
“Sai dai wani abin mamaki shi ne na yadda gwamnatin tarayya ta gurfanar da ni gaban kotu akan laifin da ni aka yi wa. Laifin da wadanda na ke zargi suna gaban kotu ba a ma yanke musu hukunci ba. Laifin da an samu hujjoji da dama na cewar an yi barazana da rayuwa.”
“In har gwamnatin Muhammadu Buhari na yin hakan ne don ta tsorata ko firgita ni na daina fadin abinda na aminta shi ne gaskiya a wannan zaure, to, sun yi kadan, domin ni bana jin tsoron garkamewa a gidan maza tunda wadanda ake rufewa a can suma mutane ne kamata.”
“Ina mai kara jaddadawa gwamnati cewa, bata isa ta rufe bakina ba, domin tsuke baki ka yi shiru a inda rashin adalci ya bayyana karara, baban laifi ne kuma cin amanar mutanen da muke wakilta ne.”
“Gwamnatin da ta gabata ta tsare ni har sau 14. Gwamnatocin Abacha da Babangida sun tsare ni. Saboda haka bana tsoron gidan yari wanda dama an gina shi don a ajiye mutane, saboda haka za mu ci gaba da tsage gaskiya komai dacinta,” Inji Melaye.
A lokacin da ya ke yin tsokaci game da wannan batu, Saraki ya bayyana kyamarsa ga yadda gwamnatin tarayya ta maka Melaye a kotu a kan wannan batu. Sai dai ya tabbatar da cewa, majalisar dattawa za ci gaba da tattauna batutuwan da suka saba da tsarin gudanar da mulki a farfajiyarta a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Ya ci gaba da cewa, jami’an gwamnatin nan da dama makiyan dimokuradiyya ne, wannan ne ma ya sanya majalisa za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da dimokuradiyya mai dorewa a Nijeriya.