
A yau Laraba ne malamai a jihar Enugu su ka bukaci gwamnatin jihar ta fara aiwatar da cikakken tsarin biyan mafi karancin albashi na kasa na naira dubu 30.
Shugaban kungiyar malamai ta ƙasa, NUT reshen jihar, Theophilus Odo, ya ce akwai buƙatar a biya malaman mafi karancin albashi sab oda su na fuskantar ƙalubale.
Ya zayyana wasu daga cikin ƙalubalen da su ka haɗa da kin karin albashi idan an samu ƙarin matsayi ; rashin biyan ma’aikata da suka yi ritaya haƙƙoƙinsu da kuma rashin ɗaukar sabbin malamai aiki.
Da ya ke jawabi a yayin gudanar da bukukuwan ranar malamai ta duniya ta 2022, Mista Odo ya jinjinawa jajircewar malaman wajen fuskantar kalubalen tattalin arziki da jihar da kasa ke fuskanta.
Ya ce bikin na bana ba wani mai armashi ba ne don haka kungiyar NUT a jihar ta yanke shawarar yin addu’o’i a maimakon yin biki.
Ya kara da cewa, taken bikin na bana: “Canjin Ilimi ya Fara da Malamai” ya nuna halin da jihar Enugu ke ciki a halin yanzu.