
Wani malamin addinin Kirista, Ekapong Ubi ya musanta cewa yana cikin waɗanda a ka ce limamai ne da suka halarci taron kaddamar da tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC a jiya Laraba.
Ubi, wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a birnin Calabar a yau Alhamis, ya ce ya yi mamakin ganin sunansa da lambar wayarsa da su ka fito a na 26 a jerin sunayen malamai da suka halarci taron da ya gudana a Abuja.
Malamin ya ce yana gidansa da ke Calabar, Cross River, lokacin da aka yi bikin kaddamar da Shettiman.
“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, ina a Mil 8, Calabar, Jihar Cross River kuma ban yi tafiya Abuja cikin watanni uku da suka wuce ba.
“Babu wani kira da wani ya yi min kuma ban sani ba kuma ni ba dan APC ba ne. Don haka sun yanke shawarar yin amfani da hakan wajen karɓar kudi ne kawai
“Ubangiji Rayayye da nake bauta wa, shi ne zai hukunta su.
“Ina kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su bi diddigin wadannan masu aikata barna domin a yi maganinsu.
“Sun sami lambata ne daga shafina na Facebook, takardun hannu, ko fosta. Na kaɗu da jin labarin nan,” in ji shi.
Da yake magana kan tikitin musulmi da musulmi, ya ce, “Nijeriya ba ta bukatar irin wannan haɗin a yanzu.”