Home Kanun Labarai Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 65 a jihar Delta

Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 65 a jihar Delta

0
Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje 65 a  jihar Delta

Daga Hassan Y.A. Malik

Mamakon ruwan sama da aka yi a daren jiya wanda ya zo tare da iska mai karfi kuma ya dauki tsawon awanni uku yana zuba kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar rushewar gidaje 65 tare da raunata mutane shida a garin Umudike da kw yankin Ossissa cikin karamar hukumar Ndokwa da ke a jihar Delta.

Shugabannin sarautar gargajiya na yankin, Cif Onotu-Uku da Cif Joseph Eloke Adibeli ne suka shaidawa manema labarai cewa, “Gidaje 65 sun rushe, haka kuma gonakin ayabar pilanten, kwakwa, barkono da sauransu na dubunnan kudi  ne syka lalace banda inji bayar da ruwan sha na yankin da shi ma ya karye ya fado duk a ruwan na jiya da dare.”

Ko a makon da ya gabata ma dai sai da irin wannan ruwan ya yi irin wannan ta’adi a garin Alifikede da ke yankin Agbor na jihar.

Cif Onotu-Uku ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Delta da su kawo dauki ga mutanen da abin ya shafa domin dai lamarin ya jefa su cikin wani mummunan hali.

Daya daga cikin wanda tsautsayin ya rutsa da su, Cif David Igbinoba ya shaidawa manema labarai cewa: “Ruwan na daren jiya ya lalata muhallinmu ta yadda a halin yanzu bamu da wurin kwana. Gidajena har guda biyu ne suka rushe sakamakon ruwan. Na gama yawo, ga tsufa ya kama ni. Ina rokon mutane da su taimaka min don ban san ta inda zan fara ba.”