
Daga Hassan Y.A. Malik
Kungiyar Manchester United ta shiga jerin sahun masu zawarcin dan wasan gaba na PSG, Neymar Junior.
Manchester United za ta kara da Real Madrid a kokarin daukar Neymar din.
Mujallar Don Balon ta rawaito cewa Neymar na son ficewa daga PSG bayan da ya koma kungiyar a karshen kakar bara a wani kwantiragi na Yuro miliyan 222 da ya sanya ya zama dan wasa mafi tsada a duniya.
Tuni dai Real Madrid ta fara zawarcin Neymar, amma Man Utd ta fito da karfinta don dauke Neymar din tare da mayar da shi jagora a kungiyar.
Rahotanni a baya-bayan nan sun bayyana cewa Neymar ya umarci mahaifinsa da ya kammala komawarsa Real Madrid kafin gasar cin kofin duniya da za a buga a shekarar nan a kasar Rasha.