Home Ƙasashen waje Ko maniyyaci bai yi allurar korona ba zai yi Hajji da Ummara – Saudiya

Ko maniyyaci bai yi allurar korona ba zai yi Hajji da Ummara – Saudiya

0
Ko maniyyaci bai yi allurar korona ba zai yi Hajji da Ummara – Saudiya

 

A jiya Litinin ne Kasar Saudi Arebiya ta share duk wasu matakan kariya da ga kamuwa da cutar corona, inda ta ce duk wani maniyyaci zai iya yin aikin Hajji ko Ummara ba tare da ya nuna shaidar yin allurar rigakafin korona ko gwajin cutar ba.

Ma’aikatar Lafiya ta ƙasar ta ce maniyyata da masu ziyara da ba su yi allurar korona ba za a bar su su shiga ƙasar da ko wacce irin biza.

Shafin Haramain ya rawaito cewa a jiyan ne ma’aikatar lafiya ta Saudiya ta sanar da cewa ta kai matakin yin allurar korona na kashi 99 cikin ɗari, inda yanayin kamuwa da cutar yayi ƙasa zuwa kashi 5 cikin ɗari.