
Da yawan manoman alkama sun yi shakulatun bangaro da batun girbin alkama a bana sakamakon rashin kasuwar alkamar a Najeriya.
Shugaban kungiyar manoman alkama na Najeriya reshen jihar Kano, Faruk Rabi’u shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai ranar Juma’a a Kano.
Yace, manoman alkama ba su da wani abun yi face su yi ko in kula da batun samar da alkama a bana, sabida yadda ake shigo da alkama daga kasar waje wanda hakan yake kara kashe guiwar manoman alkama na Najeriya.
Faruk Rabi’u ya kara da cewar, a shekarar 2017 fiye da hekta 33,000 na alkama aka shuka a jihar Kano, yace a noman rani kuwa an shuka hekta 10,000.
“Da yawan manoman alkama a jihar Kano sun dakata da samar da alkama sabida rashin kasuwar ta gida Najeriya da ake shukawa”
“Ashekarar da ta gabata, fiye da hecta 33,000 ta alkama aka shuka a jihar Kano, amma a bana hekta 10,000 kawai Manoman alkama suka iya nomawa” A cewarsa.
Shugaban kungiyar manoman alkamar ya bukaci Gwamnati da ta hana shigo da alkama daga kasar waje domin baiwa manoman alkama na Najeriya damar samun kasuwa.
Ya kara da cewar, wannan kiran nasu ya zama dole nein ba haka ba to manoman alkama na gida zasu shiga cikin tsaka mai wuya.
Ya bukaci lallai Gwamnatin tarayya ta shigo domin kawowa manoman alkama na Najeriya dauki sabida mawuyacin halin da suke ciki na rashin samun kasuwa idan sun yi noma.