Home Labarai Manoman tumatir 100 ne zasu amfana da kayan tallafin Fadama III a Daura

Manoman tumatir 100 ne zasu amfana da kayan tallafin Fadama III a Daura

0
Manoman tumatir 100 ne zasu amfana da kayan tallafin Fadama III a Daura

A jihar Katsina dake Najeriya, akalla manoman tumatir 100 ne zasu amfana da kayan tallafin noman tumatir daga sarin Fadama III na Gwamnatin tarayya domin bunkasa harkar noma a  jihar.

Shugaban hukumar dake kula da tsarin Fadama III, Alhaji Bashir Zango ne ya bayyana hakan, a lokacin da ake rabawa wadan da suka ci gajiyar kayan tallafin agarin Daura.

Yace an tsara wannan shirin ne tare da hadin guiwar Gwamnatin jihar Katsina domin tallafawa kananan manoma su bunkasa sana’arsu ta noma.

Bashir Zango ya cigaba da cewar, wadan da suka ci gajiyar wadannan kayan tallafi, sun fito ne daga kungiyoyin masu noman tumatir guda goma da ake da su a garin na Daura.

“Zamu yi kokarin fadada wannan aikin bayar da kayan tallaf zuwa ga sauran manoma na kasa”

Zango ya kara da cewar, daga cikin kayan tallafin da aka bayar, sun hada da, buhun taki 300 da maganin kwari jarka 30, da injin ban ruwa da muzurarin ruwa kusan guda 1,000 manoman suka amfana da su.

“Bayan haka kuma, mun samar da daruruwan galan galan na maganin kwari domin rabawa manoman”

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar manoman tutamir din na Daura, Bala Rabe yayi kira ga wadan da suka ci gajiyar kayan tallafin da su yi kyakkyawan amfani da su ta hanyar  da ta dace, domin bunkasar harkar noman tumatir a yankin.

Daga nan, ya bukaci matasa daa su himmata da ayyukan gona domin samun dogaro da kai da kuma habakar tattalin arziki da bunkasar hanyoyin kudin shiga a kasarnan.

NAN