
Wanda ya Rubuta Dr Abbati Bako Fassarawa zuwa Hausa Rabiu Biyora
Alhaji Audu Bako gwamnan kano na farko a zamanin mulkin soja, an haifeshi ranar 24 November 1924 a barikin yan sanda dake Kaduna, mahifinsa Malam Bako San sanda ne mao mukamin Saja wanda ya bayar da gudummawa mai yawa kafin ritayarsa.
Alhaji Audu Bako yayi karatunsa a kaduna Government School, daganan ya wuce zuwa Zaria inda yayi karatun Middle School daganan ya zarce zuwa aikin dan sanda a shekarar 1942, Audu Bako yayi karatun sanin aikin dan sanda a makarantar Metropolitan Police Training School dake Kasar Ingila a shekarar 1954, ya sake komawa ingila a shekarar 1955 inda ya samu horo akan Forensic Science Course, ya halacci karatukan kara gogewa a aikin Police a Nigeria da kasashen waje daga 1955 zuwa 1962.
Audu Bako yana daya daga cikin wakilan Nigeria da suka halacci taro a birnin Niamey na kasar Niger karkashin kungiyar Organization Of African Unity (O.A.U) wacce yanzu ta koma (AU) sun tattauna akan yadda zaa shawo kan rikicin Biafra a lokacin.
Tsohon Shugaban Nigeria Yakubu Gawon ya nada Police Commissioner Audu Bako matsayin sabon Gwamnan Kano a shekarar 1967 bayan da aka Kirkiri jihar Kano, jihar dake dauke da manyan Masarautu guda hudu, Kano, Hadejia, Gumel da kuma Kazaure dukkansu karkashin jiha daya.
Gwamna Audu Bako ya hadu kalubale masu yawa a matsayinsa na gwamnan farko a jiha mafi tasiri a kasar, musammam kasancewar jihar itace kan gaba a harkar kasuwanci da yawan mutane a kasar da kuma yankin africa na lokacin, ga kuma yakin Basasa na Biafra da ake tsaka dayi wanda ya kara haifar da babban kalubale ga jihar kano da kasar baki daya, amma duk da haka Gwamna Audu Bako yayi kokari sosai wajen samar da ayyukan alheri ga jihar tare da tsare rayukan al’umma.
Gwamna Audu Bako ana bayyana shi da jajirtaccen mutum mai hazaka tare da hangen nesa wajen yanke hukunci akan dukkan ayyukan dazai samar zamanin yana mulki, shine mutumin daya dora taswirar jihar kano wacce har yanzu baa kai ga samarwa ba kamar yadda ya tsara, a zamaninsa aka fara samar da ginin shalkwatar kananan hukumomi don matso da Gwamnati kusa da al’umma, shine ya fara samar da manyan tituna masu hannu biyu tare da fitulu a cikin birnin kano da kuma kananan hanyoyi a kauyuka don temaka manoma samun hanyar fito da kayan noma zuwa kasuwanni, ya gina manyan Dams duk don inganta noman rani, ya samar da guraren shakatawa dana tarihi a jihar kano duk saboda masu yawon bude ido da suke ziyartar Nigeria, shine wanda ya gina Gidajen Maaikata dake Unguwar Kundila, Zoo Road, Gwammaja da kuma Ja’oji dake kan titin zaria Road.
Shine ya gina Titin Ibrahim Taiwo, State Road, Murtala Muhammad Way, Ahmadu Bello Way, Audu Bako Way.
Ya Gina Gidan Murtala gini mafi tsawo a yankin Arewa gaba daya a wancan lokacin, ya gina ginin Kano High Court, Magwan Water Restaurant, Thomas College Of Agriculture, Mallam Kato Square, African House dake cikin Gidan Gwamnatin Kano, duk ya samar da wadannan ayyukan cikin mukinsa na shekara takwas.
Gwamna Audu Bako ya kafa tarihi mai wahalar rushewa a jihar Kano, yayi aiki tukuru wajen inganta harkar ilmi lafiya, hatta bangaren wasanni sun samu gata na musammam a zamanin mulkinsa, wanda hakan yasa a yanzu aka sanyawa gurare masu yawa sunansa a jihar kano, ake kara mutumta shi bisa hobbasar da yayi wajen inganta jihar kano da kanawa, ya samar da maaikatar kula da ruwansa mai tsafta a jihar kano maisuna WRECA wanda ke samar da tsaftataccen ruwa ga al’umma.
Marigayi Gwamna Audu Bako yayi ayyukan da bazaa taba mantawa dashi ba.