Home Labarai Marubuci ɗan Nijeriya, Saddiq Dzukogi, ya koka kan cin zarafin sa Amurka

Marubuci ɗan Nijeriya, Saddiq Dzukogi, ya koka kan cin zarafin sa Amurka

0
Marubuci ɗan Nijeriya, Saddiq Dzukogi, ya koka kan cin zarafin sa Amurka

Wani marubuci kuma malami dan Nijeriya mazaunin kasar Amurka, Saddiq Dzukogi, ya koka kan cin zarafi da ƴansandan jihar Mississippi ke yi masa a Amurka.

Dzukogi, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a jiya Laraba, ya ce lamarin na baya-bayan nan shi ne na biyu cikin jerin hare-haren wariyar launin fata da ‘yan sanda suka kai masa.

Dzukogi, wanda mataimakin farfesa ne a Jami’ar Jihar Mississippi, duk da haka, ya nuna godiya ga Allah cewa ya tsallake hare-haren ba tare da lafiyarsa ta taɓu ba.

Ya rubuta cewa, “Wannan shi ne karo na biyu a wannan shekara da ƴansanda a Mississippi ke cin zarafi ma ba tare da wani dalili ba sai don kawai ni bakar fata ne.

“Na farko, yayin da nake yawo a unguwarmu sanye da kayan bacci, sai kuma a a yau, a na je ganin wani likita. Na gode dai ina cikin koshin lafiya kuma rayuwata har yanzu tawa ce.