
Kwamitin gudanarwa na babban masallacin ƴan-majalsu da ke Abuja, ya nada Sheikh Sufyan Malumfashi a matsayin sabon babban limamin masallacin.
Sakataren kwamitin kula da masallacin, Mansur Jarkasa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau0 Lahadi a Abuja, inda ya ce nadin ya fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Fabrairu.
Nadin ya zo ne kimanin watanni 10 bayan sallamar Sheikh Muhammad Nuru Khalid (wanda aka fi sani da Digital Imam) a matsayin babban limamin masallacin a watan Afrilun 2022, bayan ya soki gwamnatin Buhari kan rashin tsaro da wahala.
A cewar Jarkasa, sabon nadin ya samu amincewar kwamitin gudanarwa na masallacin, karkashin jagorancin Saidu Dansadau da mataimakinsa, Abubakar Bawa Bwari.
Ya ce kwamitin “bayan duk binciken da ya dace, da tuntubar masu ruwa da tsaki da bin ka’ida suka yanke shawarar nada Sheikh Sufyan Malumfashi baki daya a matsayin sabon babban limamin masallacin.”
Jarkasa ya ce Malumfashi ya taba zama babban limamin masallacin Juma’a na Area 11, kuma ya kasance a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Asokoro a matsayin limamin sallar Juma’a.
Sakataren ya ce a halin yanzu Malumfashi limamin Juma’a ne na masallacin Al-Noor, Wuse II, duk a Abuja.