Home Siyasa Ba mu da masaniyar jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu — Onanuga

Ba mu da masaniyar jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu — Onanuga

0
Ba mu da masaniyar jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu — Onanuga

 

Kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya ce ba shi da masaniyar jerin sunayen da ake yaɗa wa a shafukan sada zumunta da wallafa wasu a kafafen yaɗa labarai na yanar gizo.

Daraktan yaɗa Labaran Kwamitin, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Asabar a Abuja, inda yace an wallafa wanɗannan sunayen ne ba da izinin kwamitin ba.

Ya buƙaci jama’a da su yi watsi da jerin sunayen, inda ya ƙara da cewa shugabancin jam’iyyar da dan takararta na shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu za su ƙaddamar da cikakken kwamitin yaƙin neman zaɓen nan gaba, a hukumance.

Onanuga ya ce sun fahimci al’umma na kaunar jam’iyyar APC, shi yasa ma su ka ƙagu su san su waye ƴan kwamitin yaƙin neman zaben dan takararsu na shugaban ƙasa.

Sai dai ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su yi takatsantsan wajen yada labaran da ba su dace ba.

A lokacin da yake zantawa da sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Mista James Faleke, Onanuga ya ce ana ci gaba da samar daraktoci daban-daban na tsarin yakin neman zaben.

Ya ce ana yin hakan ne tare da tuntubar gwamnonin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar don yin abun da ya dace.