Home Siyasa 2023: Ba mu da masaniyar kundin rahoton cewa za mu kashe tiriliyan 6.5 don sayen ƙuri’u — APC

2023: Ba mu da masaniyar kundin rahoton cewa za mu kashe tiriliyan 6.5 don sayen ƙuri’u — APC

0
2023: Ba mu da masaniyar kundin rahoton cewa za mu kashe tiriliyan 6.5 don sayen ƙuri’u — APC

 

 

 

Jam’iyyar APC ta yi watsi da wani kundin rahoto da ya bayyana cewa ta tanadi naira tiriliyan 6.5 domin sayen ƙuri’u don tabbatar da samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Felix Morka, Sakataren Yad5a Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin a Abuja, ya bayyana rahoton a matsayin na bogi, inda ya ce aiki ne na masu yarfe.

“Hankalin jam’iyyar APC ya kai kan wani kundin rahoto da ke yawo, mai taken Kundin Zaɓen APC na 2023 da a ka fallasa.

“A wani salo na sharri, kundin ya yi zargin cewa jam’iyyarmu ta tanadi zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan 6.5 don samar da tsare-tsare da nufin rarraba wa ƴan Najeriya wajen zaɓen jam’iyyar da ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2023.

“Abin dariya ma, takardar ta yi zargin cewa an tanadi wasu maƙudan kuɗaɗe don sayen ƙuri’u kai tsaye, ta amfani da ma’aikatan INEC, jami’an tsaro, jami’an shari’a da sauran jami’ai.

“Jam’iyyar APC na son a tabbatar da cewa kundin ba na jam’iyyar ba ne. Ba mu rubuta ko mallaki irin wannan kundi ba, kuma ba daga jam’iyyarmu ya fito ba,” in ji Mista Morka.

Ya ce kundin da a ke magana a kai, aiki ne na jam’iyyar adawa ta PDP a kokarin da take yi na ganin an yi zaɓe da sahihi ba, ta hanyar ƙoƙarin ɓata wa jam’iyyar APC suna.