Home Labarai Masari ya baiwa Rarara da Baban Chinedu kyautar Naira miliyan 80 bayan an ƙona musu gidaje da ofis

Masari ya baiwa Rarara da Baban Chinedu kyautar Naira miliyan 80 bayan an ƙona musu gidaje da ofis

0
Masari ya baiwa Rarara da Baban Chinedu kyautar Naira miliyan 80 bayan an ƙona musu gidaje da ofis

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya gwangwaje mawakan APC din nan, Dauda Kahutu Rarara da Yusuf Baban Chinedu da kudi har Naira miliyan 80.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa bayan zaɓen gwamnan Kano, rahotanni sun bayyana cewa wasu ɓata-gari sun kona gida da ofishin mawakan a jihar Kano.

Sai dai kuma hakan na neman zamar musu gobarar-titi, bayan da rahotanni su ka bayyana cewa Masari ya basu kyautar miliyan 80 domin su sayi wasu gidajen.

A wata wasika mai ɗauke da sa hannun wani Saminu Soli, a madadin Kwamishinan Kasafin kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, gwamnan ya baiwa Rarara Naira miliyan 50, inda Baban Chinedu ya samu Naira miliyan 30.

A wasikar, mai ɗauke da kwanan wata 5 ga Mayu, mai lamba MBEP/BD/REC/FA/23/VOL.I/1044, an yi kwarin ta zuwa Sakataren Gwamnatin jihar.

Wasikar ta ce an basu kudaden ne domin su samu wasu gidajen da za su ajiye iyalan su bayan koma musu nasu da aka yi a Kano.