
Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a jiya Talata ya zubar da hawaye yayin da ya ke gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2023 na N288,633,257,963 ga majalisar dokokin jihar.
Gwamnan ya shaida wa majalisar cewa kasafin kudin na nufin kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma kaddamar da wasu sabbi da za a kammala a wa’adin gwamnatinsa a jihar.
Sai dai a lokacin da ya ke gabatar da kudirin kasafin kudin, sai a ka ga gwamnan na zubar da hawaye, yana mai cewa wannan shi ne karo na karshe da zai gabatar da kasafin kudin ga majalisar.
Ya ce, “Kamar yadda ku ka sani, wannan shi ne karo na karshe da zan tsaya a gaban masu girma ƴan majalisar dokokin jihar Katsina domin gabatar da daftarin kasafin kudin gwamnatin jihar Katsina,”
Gwamnan, wanda ya fara duba kasafin kudin shekarar 2022, ya ce ayyukan sa sun zarce matsakaicin mataki.