Home Siyasa Masu riƙe da muƙaman siyasa za su sauka kwanaki 30 kafin zaɓe — kotu

Masu riƙe da muƙaman siyasa za su sauka kwanaki 30 kafin zaɓe — kotu

0
Masu riƙe da muƙaman siyasa za su sauka kwanaki 30 kafin zaɓe — kotu

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Umuahia a jihar Abia ta umarci babban lauyan Gwamnatin tarayya Kuma ministan Shari’a da ya gaggauta soke sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Mai shari’a Evelyn Anyadike, a yau Juma’a ta ce sashin ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar, ba ya kan ka’ida, kuma ya ci karo da tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Sashen yana cewa: “Babu wani nadadde da Zai zaba ko a zabe shi a Wani mukami a cikin jam’iyyar ba tare da ya ajiye mukamin sa ba kwanaki 30 kafin zabe”.

A cikin karar mai lamba FHC/UM/CS/26/2022, Mai Shari’a Anyadike ya kara bayyana cewa sashe na 66 (1) (f), 107 (1) (f), 137 (1) (f) da 182 (1) (f) ) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya rigaya ya bayyana cewa masu Nadaddu a mukaman Gwamnati da suke son tsayawa takara zasu sauka daga Kan mukaminsu akalla kwanaki 30 kafin ranar zabe kuma duk wata doka da ta tilasta wa wadanda aka nada su yi murabus ko barin ofis a kowane lokaci kafin hakan ta saba wa kundin tsarin mulki.

Yayin da yake rattaba hannu kan kudurin dokar zabe a watan da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar kasar nan da ta soke sashe na 84 (12), bisa dalilan rashin baiwa Masu rike da muka Mai hakkinsu .
Sai dai majalisar dattawan ta ki yin la’akari da bukatar shugaban kasar kuma ta yi watsi da kudirin na neman a yi wa sashen kwaskwarima.