
Babban Sakataren Hukumar Kula da Nakasassu ta Ƙasa (NCPWD), James Lalu, ya zargi Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, da nuna halin rashin kula wa ga nakasassu (PWD).
A baya dai Atiku ya bukaci nakasassu da kada su zabi jam’iyyar APC a zaben 2023.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi jam’iyya mai mulki da gaza aiwatar da dokar nakasassu duk da amincewar majalisar dokokin kasar.
Sai dai kuma jaridar TheCable ta rawaito cewa da ya ke magana a taron manema labarai a jiya Alhamis, Lalu ya ce lokacin da Atiku ya ke mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, bai tsinana wa nakasassu komai ba.
Ya ce jihohin PDP ba su aiwatar da dokar masu buƙata ta musamman ba , yayin da jihohi irin su Plateau, Legas, Nasarawa, Zamfara, Kogi, Jigawa da sauran da dama da APC ke mulki sun yi nisa a cikin aiwatar da dokokin.
Ya ce tun da Buhari ya hau mulki a kodayaushe ya na nuna damuwa da muradin nakasassu.
“A wa’adin farko da na biyu na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP, nakasassu sun yi ta kokawa, ko da majalisar dokokin kasar ta amince da kudirin, Atiku da PDP ba su sanya hannu kan dokar ba,” in ji Lalu.
“Har yanzu zan iya tuna wa lokacin da nakasassu su ka fito zanga-zangar su ka ja hankalin gwamnatin wancan lokacin, amma sakamakon kawai da muka samu shi ne a ka fesa mana hayaki mai sa hawaye.
“A koyaushe za mu yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari. Shi ne babban abokin al’ummar masu buƙata ta musamman .
“Lokacin da ya hau mulki, ya samu damar sauraron koken mu. A shekarar 2014 a Lafia, Buhari a lokacin yakin neman zabensa, ya yi alkawarin sanya hannu kan kudirin nakasassu ya zama doka.
“A ranar 17 ga Janairu, 2019, Buhari ya rattaba hannu kan dokar haramta wariya ga nakasassu. A ranar 17 ga Agusta, ya amince da nadin hukumar gudanarwar ta nakasassu.