Home Labarai Masu kada kuri’ah a Masar sun nuna sha’awar zaben Muhammad Salah a matsayin Shugaban kasa

Masu kada kuri’ah a Masar sun nuna sha’awar zaben Muhammad Salah a matsayin Shugaban kasa

0
Masu kada kuri’ah a Masar sun nuna sha’awar zaben Muhammad Salah a matsayin Shugaban kasa

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Masu kada kuri’a a kasar Masar da dama ne suka zabi dan wasan kasar da yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah a matsayin sabon shugaban kasar su a zaben shugaban kasar da akayi a wannan satin.

Masu kada kuri’a da dama ne dai suka lalata kuri’arsu sannan kuma suka rubuta sunan Muhammad Salah a matsayin wanda suke so ya zama shugaban kasarsu duk da cewa baya cikin yan takarar da suke neman shugabancin kasar.

Salah, mai shekaru 25 ya zura kwallaye 35 cikin wasanni 55 daya bugawa kasar ta Masar ciki har da kwallon daya zura a ragar kasar Congo kuma kwallon ce tabawa kasar tasa damar zuwa gasar cin kofin da za’ayi a Rasha.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana akwai kuri’a sama da miliyan daya da masu kada ta suka lalata kuma duk sun rubuta sunan Salah a bayan kuri’ar.

Salah dai shine yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a gasar firimiyar kasar ingila inda ya zura kwallaye 29 bayan da kungiyar ta Liverpool take mataki na uku sannan kuma har yanzu kungiyar tana buga gasar zakarun turai.

Abdel-Fattah Al-Sisi ne ya lashe zaben kasar ta Masar da kasha 92 cikin dari na kuri’un da aka kada.