Home Labarai Masu tsukakkiyar fahimta ne zasu kasa fahimtar fatawar Dr. Sani Rijiyar Lemo

Masu tsukakkiyar fahimta ne zasu kasa fahimtar fatawar Dr. Sani Rijiyar Lemo

0
Masu tsukakkiyar fahimta ne zasu kasa fahimtar fatawar Dr. Sani Rijiyar Lemo
Daga Aliyu Muhd Sani
Kwana biyu da suka wuce ne wani mutum ya tayar da hayaniya a kan Fatawar da daya daga cikin manyan Malamanmu na Sunna ya bayar, Fatawar da aka yi masa a kan wanda ya yi zina da mace, sai daga baya ta bayyana cewa; matarsa ce.
Shi wancan mutumi ya zo Facebook ya yi ta hayaniyarsa a kan Fatawar, in da ya ce: Fatawar da Malam ya bayar kuskure ce, alhali ba tare da ilimi ba, kawai bisa hayaniya da ya saba yi.
To ni lokacin da na fara ganin maganar, na yi fatan Allah ya sa kar a kula shi, saboda wasu dalilai kamar haka:
1- Kawai neman suna yake yi, a ce: yau ga shi yana raddi ga babban Malaminmu Dr. Sani.
2- ‘Yan Boko Akeeda so suke yi su zama su suke jagorancin tattaunawa a Facebook, ta hayar tayar da hayaniya, sai gaba daya mutane su raja’a kansu.
Wannan ya sa duka za ka sami kowannensu Dan Hayaniya ne (Controversial). Wannan kuma babbar hanya ce ta yada barnarsu. Mutum da gangan ya zama mai tayar da hayaniya da cece-kuce, saboda da haka za suna jan hankalin jama’a gare su, suna yada manufofinsu.
To amma saboda kasancewar Manhaji ne na Ahlus Sunna, Manhajin da ya zama musu dabi’a da al’ada, ba su iya yin shiru a kan barnar mabarnaci, don haka aka yi ta yi masa raddi daban – daban.
To ni tun asali ban so na ce komai ba, amma saboda Malam ya yi cikakken bayani a kan Fatawar, ya haska wa mutane jahilcin wancan dan hayaniyar, to sai na so na kara haska wa mutane Manhajin irin wadannan ‘Yan Hayaniya.
Asalin wannan Manhaji shi ne Manhajin ‘Yan Boko Aqeeda, Manhaji ne da ya ginu a kan yakar Addini ta hanyoyi masu yawa, daga ciki:
1- Zare wa Nassin Addini, musamman Hadisan Annabi (saw) tsarki da daraja, da nuna cewa; ba su da wata kariya a karan kansu. Wannan ya sa za ka ga sun zo suna wulakantar da Hadisan Sahihul Bukhari da Muslim, suna watsi da su, suna watsi da Sahabban da suka ruwaito su, musamman Abu Huraira (ra).
2- Wasa da nassoshin Addini da fassarar su bisa son rai, don su bi rayuwar zamani, wacce ake kira rayuwar Turai. Tare da watsi da fassarar magabata ga Nassoshin, da raya cewa; fassararsu ba za ta dace da wannan zamani ba.
3- Wulakantar da tabbatattun mas’alolin Addini, na Aqida da Shari’a, wadanda ake kira da Larabci (الثوابت), da mayar da su tamkar mas’alolin Ijtihadi, wadanda babu laifi a yi sabani cikinsu, da ba wa kowa ‘yancin zabin abin da ya dace da son ransa.
4- Sakulanci, wato raba Addini da harkokin rayuwa, da takaita Addini a Masallaci, da kuma mayar da shi ya zama alaka tsakanin bawa da Ubangijinsa kawai, ban da abin da ya shafi sauran fagagen rayuwar jama’a ta yau da kullum.
5- Cire wa mutane Akidar “Wala’i da Bara’i”, wato Akidar son Muminai da kin Kafirai, da nuna cewa; kafirai da Musulmai duk daya suke. Kai, har ya kai ga wani daga cikinsu yana fifita wata Kafira Baturiya ‘yar fim a kan Sahabin Annabi (saw).
6- Karfafa Bidi’o’i da ‘yan Bidi’a. Da ma su din ma su ne, sai dai su nasu Bidi’a ce da kari. Saboda duka za ka samu ‘Yan Bidi’o’in Sufanci da Shi’anci ne, saboda babu mai shiga wannar harka ta Boko Aqeeda sai wanda Nassin Alkur’ani da Hadisan Annabi (saw) da Sahabbansa ba su da girma da daraja a cikin zuciyarsa.
7- Wannan ya sa suke inkarin Jihadi, kuma suke nuna kiyayya ga Ahlus Sunna da siffanta su da ‘Yan Ta’adda, ba don komai ba, kawai saboda tsantsanr kiyayya da yakar masu riko da Addini.
8- Kokarin jefar da haddi na Shari’a, kamar haddin zina, ridda da sauransu, duka da sunan ‘yanci da kare hakkin bil’adama. Hatta inkarin wannar Fatawar yana da alaka da wannan.
9- Amfani da dabaru da wasa da Nassoshi da kuma dauko ra’ayoyi “shazzai” don halasta haramun, da wulakantar da Sunnoni, duka da sunan sauki wa al’umma, alhali kokari ne na raba ta da hakikanin Addininta.
10- Wannan ya sa suke tsangwaman masu riko da Addini, masu wa’azi da da’awa da kira ga Sunna, masu umurni da kyakkyawa da hani ga mummuna, suke kiransu da masu tsattsauran ra’ayin Addini.
11- Rena Malamai Masana Addini da Sunna, da kokarin tozarta su, da zubar da kimarsu, su kuma su nada kawunansu a matsayin Malamai masu bayar da Fatawa, don su isa ga manufarsu. Wannan shi ne abin da ya faru game da wannar Fatawa.
12- Kira ga mace don ta fandare, ta cire hijabi, ta fito titi a fantama da ita.
13- Kira ga matasa maza da mata su shiga rayuwar holewa da jefar da riko da Addini da kyawawan halaye da dabi’u.
Wadannan a takaice kenan, amma suna da yawa, na kawo su ne  a dunkule a matsayin Manhaji da suke tafiya a kai, duk mai kallon irin rubuce-rubucensu ya san misalai masu yawa a kan wadannan abubuwa da muka jero.
Saboda haka wadannan matasa ‘Yan Boko Akeeda, wannan shi ne Manhajinsu, suna nuna sanin Addini, alhali karya suke yi. Kuma da ma dole su yi wannar karyar, saboda in ba su nuna haka ba, babu wanda zai saurare su a maganar Addini, amma a bisa hakika jahilai ne. Ai yanzu kam kowa ya tabbatar da haka, a wannan garajen da daya daga cikinsu ya yi, a Fatawa da muke magana a kanta.