Home Labarai Mata 2,131 na dauke da cutar kanjamau a cikin 38,791 a jihar Legas

Mata 2,131 na dauke da cutar kanjamau a cikin 38,791 a jihar Legas

0
Mata 2,131 na dauke da cutar kanjamau a cikin 38,791 a jihar Legas

Daga Hassan Y.A. Malik

Kwamishin lafiya na jihar Legas, Dakta Jide Idris ya bayyana cewa akalla mata masu juna biyu guda 2,131 ne aka samu dauke da cutar nan mai karya garkuwar jiki a wani shiri da ma’aikatar ta yi na gwada mata masu dauke da juna biyu a jihar.

Kwamishinan ya fitar da wannan sanarwa ce a wata sanarwa da ya fitar a ma’aikatar lafiya ta jihar da ke da shedikwata a a Alausa, cikin Ikeja,babban birnin jihar, inda ya bayyana cewa a shekara guda da ta gaba akalla ma’aikatar lafiya ta yi gwajin cutar kanjamau akan mata masu dauke da juna biyu guda 38,791 kuma daga cikin wannan adadi an samu mata 2,131 dauke da cutar.

“Jihar Legas ta aiwatar da zango na farko na yaki da cutar da kanjamau, kuma jihar ta yi amfani ne da kudaden da ta karba daga majalisar dinkin duniya don yin yaki da cutar.

“Wannan zango na gwaji da gwamnatin Legas ta gudanar ya samu nasara, kuma sauarn sassa na duniya za su dauki jihar Legas a matsayin misalin yadda za su yaki cutar kamar dai yadda gidauniyar yaki da cutar ta duniya ta yi umarni.

“Zango na farko na yaki da cutar kanjamau din ya dauki tsawon lokaci tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2017, inda jihar ta yi amfani da kudaden da ta samu don aiwatar da aikin da adadinsu ya kai Dalar Amurka miliyan tara da dubu dari shida da ashirin da uku da dari uku da casa’in da digo sifili takwas, wajen gudanar da tantance masu nuna biyu a kananan hukumomi 3 da ke karamar hukumar, yi musu gwaji tare da samar musu da tallafin magunguna da sauran abubuwa da lafiyar mai dauke da cutar ke bukata.

“Jihar Legas ta yi amfani da kaso 10 cikin 100 na tallafin da ta samu don aiwatar da aikin gwajin tare kuma da aiwatar da ayyukan wayar da kan al’ummar jihar akalla mutum 226,768 akan cutar tare da basu ilimin yadda za su kula da kansu idan har sun dauki cutar.

“Haka kuma, mata masu juna biyu guda 38,791 sun san san matsayin dangane da akwai ko rashin cutar kanjamau, inda aka samu mata 2,131 dauke da cutar kuma tuni aka daura a tsarin yadda za a kare ‘ya’yan da ke cikinsu daga daukar cutar kai tsaye daga iyayensu,” Dakta Jide ya bayyana.