
Wata malamar makaranta, mai suna Joy Eze, a yau Alhamis ta maka mijinta Nuel Chukwu a gaban kotun gargajiya da ke Jikwoyi, Abuja, sabo da ya ƙi cin abincin da take dafawa, bisa zargin ta da yunƙurin sanya masa guba.
Eze wacce ke zaune a Jikwoyi, Abuja, ta yi wannan zargin ne a cikin takardar ƙorafin neman kashe aurenta da ta miƙa wa kotun a mijin nata Chukwu.
“Ba zan iya ci gaba da zama a karkashin rufin daya da wannan mutumin ba. Ya daina cin abincina, da na same nai masa magana, sai kawai ya kada baki ya ce wai yana sane da shiri na na kashe shi.
“Ya kuma gaya wa danginsa cewa idan ya mutu a kama ni,” in ji ta.
Ta kuma shaida wa kotun cewa Chukwu ya sanya ƴaƴansu sun tsane ta.
“Mijina ya je ya na ta ɓata ni a idon yaran nan. Har ce musu ya ke ni karuwa ce. Ya shaida musu cewa duk kayan da nake sawa da takalma wai samari na ne su ka siya min,” inji ta.
Don haka ta roƙi kotu da ta raba auren ta kuma ba ta rikon ƴaƴanta.
Wanda ake karar, direban babur mai ƙafa uku, wanda ya halarci kotun, ya musanta dukkan zarge-zargen da ta faɗa.
Alkalin kotun, Labaran Gusau ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 21 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraren ƙarar.