Home Wasanni Mata sun fara gudun yada kanin wani a kasar Saudiyya

Mata sun fara gudun yada kanin wani a kasar Saudiyya

0
Mata sun fara gudun yada kanin wani a kasar Saudiyya

A karon farko a tarihi kasar Saudiyya ta karbi bakuncin wasan gudun yada kanin wani na mata a karshen makon da ya wuce. Kafofin yada labarai suka ce, a kokarin ganin kasar Saudiyya ta tafi da zamani, sannan ta inganta shirin wasanni na mata ya sanya ta karbi bakuncin wannan gasa.

Daruruwan mata ne cikin shigar da bata bayyana tsiraicinsu ba, shiga irin wadda ta dace da addini suka sheka a guje a Gabashin birnin Alh-Ahsa a ranar Asabar din da ta gabata domin soma wannan wasan gudun yada kanin wani.

“Makasudin wannan wasan tseren mata shi ne, bunkasa wasan guje guje a tsakanin mata, domin samun lafiyar jiki” Gidan talabijin mallakar kasar Saudiyya na Al-Arabiya shi ne ya ruwaito mai lura da wasan Malek Al-Mousa yana fadin haka.

Wannan kuwa yana zuwa ne bayan da birnin Riyadh ya taba karbar bakuncin wani wasan mai kama da wannan a watan Fabrairu. Inda ‘yan asalin kasar Saudiyya suka yi ta yin korafi a shafukan sada zumunta na intanet, inda suke kiran lallai ya kamata a sanya mata cikin shirin wasan domin su motsa jiki.

Haka kuma, Shugabannin hukumar gudanar da wannan wasa na gudun yada kanin wani, sun shirya gudanar da wani wasanirin wannan a birnin Makkah mai tsarki a 6 ga watan Afrilun wannan shekarar, a cewar wata jaridar kasar.

Sai dai da yawan wasu ‘yan kasar ta Saudiyya sun caccaki wannan wasa na gudun yada kanin wani a kafafen sada zumunta na intent, inda da dama suke ganin hakan bai dace ba, almubazzaranci ne hukumomin kasar su ware kudade domin wannan wasan guje guje.