
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, ya shawarci mata da su yi tawaye su karɓi mulki sabo da maza sun dade suna mulki a Nijeriya.
Sowore, ɗan gwagwarmaya, ya bayyana haka ne a jiya Lahadi a yayin taron muhawarar ƴan takara zagaye na biyu da Arise TV tare da haɗin gwiwar Cibiyar Dimokaradiyya da Ci Gaba (CDD) su ka shirya.
Sowore ya ce mata sun dade da yadda da mamayar da maza su ka yi a harkar mulki a Nijeriya duk da cewa sun fi maza yawa a kasar.
Ya ce, “Akwai mata da yawa a kasar nan da suka fi maza cancanta da a zaɓa. Yaushe mata za su tsayar da mace, su kuma zaɓe ta, sannan su tilasta wa maza su zabi mace? Hakan zai magance wannan matsala ta daidaito a lokaci guda.”
“Abin da ya sa na ce wannan, Nijeriya na da ma’aikatar harkokin mata amma ban taba jin ma’aikatar harkokin maza ba.
“Akwai wani lokaci, ina tsammanin a birnin tarayya lokacin da wani mutum ke neman a zabe shi a matsayin shugaban mata na jam’iyya. A jihar Adamawa kwamishina mai kula da harkokin mata namiji ne.”
Dan takarar shugaban kasa na AAC ya ci gaba da cewa, rashin adalci ne mata su gamsu da kashi 35 cikin 100 da ake ware musu na wakilci a gwamnati, inda ya yi kira gare su da su tashi su yi tawaye dan neman kaso daidai da na maza.