Home Siyasa Mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna ya lashe zaɓen fidda-gwani

Mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna ya lashe zaɓen fidda-gwani

0
Mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna ya lashe zaɓen fidda-gwani

 

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben 2023 a jihar bayan ya lashe zaɓen fidda-gwani.

Gawuna ya samu kuri’u 2,289 inda ya kayar da abokin hamayyarsa tilo, Sha’aban Sharada, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kano Municipal, wanda ya samu kuri’u 30.

Jami’i kuma shugaban kwamitin zaɓen na jam’iyyar APC, Tijjani Kaura, ya bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar a daren jiya Alhamis a rukunin filayen wasanni na da ke filin wasa na Sani Abacha, Kano.

Ya ce jimillar kuri’u 2,339 aka kada, yayin da kuri’u 2,319 suka zama ingantattu.

Kaura ya yabawa jami’an tsaro da ‘yan jarida da ’yan takara da shugabannin jam’iyyar bisa yadda su ka taimaka a ka gudanar da atisayen cikin lumana.