
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Nasiru Ma’azu Magarya, ya ce Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau ya aikata wasu lokuta guda takwas da su ka cancanci a tsige shi.
Nagarta ya shaidawa manema labarai a Zamfara cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya amince a tsige wanda ya aikata irin irin waɗannan laifukan.
Ya ce tuni mambobin majalisa sun gabatar da ƙudirin cewa a tsige shi bisa wasu dalilai.
Ya ƙara da cewa majalisar za ta zauna ta yi nazari kafin ta aiwatar da hukunci na gaba.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa shirin tsige Mahdi ba ya rasa nasaba da ƙin komawar mataimakin gwamnan zuwa jam’iyyar APC bayan da Gwamna Bello Matawalle ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC ɗin, lamarin da ya haifar da rikici a tsakanin su.