Home Siyasa Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kano ya fice daga APC zuwa NNPP

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kano ya fice daga APC zuwa NNPP

0
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kano ya fice daga APC zuwa NNPP

 

 

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya sauya sheƙa da ga jam’iyyar APC mai mulki zuwa ta NNPP.

Massu, wanda kuma ɗan siyasa ne na asali a yankin Kano-ta-Kudu, ya bayyana matakinsa na ficewa daga jam’iyyar APC ne a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓar Massu a Ƙaramar Hukumar Sumaila a jiya Alhamis.

Ɗan majalisar ya ɗora alhakin ficewarsa da ga APC a kan rigingimun da ke faruwa a jam’iyyar, da kuma rashin adalci da rashin tsarin dimokuradiyyar cikin gida.

“Bayan abubuwan da suka faru a jam’iyyar a baya-bayan nan tare da tuntubar jama’a da magoya bayana da masu ruwa da tsaki a Sumaila da kuma Kano-ta-Kudu gaba ɗaya, na rubuta wannan wasiƙa domin sanar da ku aniya ta da yanke shawarar yin murabus da ga zama ɗan jam’iyar APC.

“An yanke shawarar ne saboda rashin adalci, rashin aiwatar da dimokuradiyya na cikin gida da kuma yadda jihar Kano-ta-Kudu ta zama saniyar ware da ga samun dimbin damammaki,” in ji shi a cikin wasikar.