
Likitocin da suka yi wa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo aiki, domin magance ciwon da ya samu a kafarsa da ya yi ta fama da shi, sun kammala aikin, inda suka bayyana cewa an yi nasara.
Mai magana da yawun Osinbajo, Mista Laolu Akande, ne ya fitar da wata sanarwa daga asibitin, inda ya tabbatar da cewa an yi nasarar yi wa mataimakin shugaban kasar ya yi nasarar aikin kafarsa a jiya Asabar a asibitin Duchess International Hospital, GRA, Ikeja, Legas.
“an kwantar da Mataimakin shugaban a asibitin Duchess International Hospital, GRA, Ikeja, Legas, a yau, saboda karaya da ya samu a kashin cinyarsa ta dama, mai yiwuwa yana da alaka da wani dogon rauni da ya dade yana fama da shi da ke da alaka da wasan squash.
“wata tawagar kwararrun likitoci, da suka hada da Dokta Wallace Ogufere, babban ƙwararren likita a fannin kashi, Dokta Om Lahoti, babban ƙwararren likita a bangaren kashi da kuma Dokta Babajide Lawson, babban ƙwararren likita.
“Sauran su ne Dokta Ken Adegoke, babban ƙwararren likita a bangaren Anesthesia da Kulawa mai Mahimmanci, Dokta Oladimeji Agbabiaka, Likitan Anesthetist da Dokta Adedoyin Dosunmu-Ogunbi, babban ƙwararren likita kuma Daraktan Lafiya.
“aikin ya samu nasara kuma ana sa ran sallamar Osinbajo cikin ƴan kwanaki masu zuwa,” in ji Mista Dosunmu-Ogunbi.