
Hassan Y.A. Malik
Mataimakiya ta musamman ga Shugaaba Muhammadu Buhari akan harkokin kafofin yada zumunta, Lauretta Onochie, ta kare mai gidan nata bisa ra’ayinsa na halartar daurin auren ‘yar gwamnan Kano, Hajiya Fatima Ganduje da angonta, Idris Ajimobi, dan gwamnan jihar Oyo, da aka yi a yau Asabar.
Onochie, a shafinta na twitter ta bayyana cewa, shugaba Muhamadu Buhri dai ba karamin yaro bane, a saboda haka yana da ikon ya zabi inda ya ke son ya je a kuma lokacin da ya ke so ya je.
An daura auren ne a Kano yau Asabar, inda shugaba Buhari da gwamnonin Nijeriya guda 22 suka halarci daurin auren.
Shugaban majalisar dattijan Nijeriya, Bukola Saraki da jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu sun halarci taron.
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya kalubalanci taron daurin auren, inda ya bayyana cewa kamata ya yi a ce shugaba Buhari ya fi damuwa da halin rashin zaman lafiya da tashin hankali da kasar ke ciki a maimakon shagalin bikin auren da shugaba da gwamnoni suke yi.