
Matan tubabbun mayakan Boko Haram sun haifi jarirai 263 a cikin watanni hudu.
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri a jiya Talata.
Matan sun haihu ne a cibiyar lafiya da ke cikin sansanin ƴan gudun hijira da ke Maiduguri, wanda a halin yanzu ake amfani da shi a matsayin mafaka na wucin-gadi ga tubabbun ‘yan ta’adda.
A cewar gwamnatin jihar, sama da ‘yan ta’addan da suka tuba 16,000 ne aka tsugunar da su a sansanin.
Da ya ke bayar da bayani ga manema labarai, jami’in lafiya da ke kula da cibiyoyin na lafiya, Dokta Mohammed Saleh ya ce an haifi yara 94 a watan Yulin 2022, 98 a watan Agusta, 60 a watan Satumba, 11 kuma a watan Oktoba.
“Kusan a kowace rana, muna karɓar haihuwa,” in ji Saleh.
Ko da yake bai bayar da alkaluman matan da suka haihu a watan Nuwamba ba, Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa akalla mata 20 ne aka ce sun haihu a cikin makonni biyun da suka gabata, daga cikinsu akwai wata mace mai shekaru 20 da ta haifi tagwaye.